fbpx
Monday, September 27
Shadow

Yanzu-Yanzu: Tsohon dan majalisar Yobe da wasu mutane sun koma APC

Tsohon dan majalisar dokokin jihar Yobe, Alhaji Audu Babale ya sauya sheka tare da daruruwan magoya bayansa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Damaturu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Babale ya wakilci Mazabar Goya/Ngeji a Karamar Hukumar Fika.

Sanarwar da Hussaini Mai-Suleh, Sakataren Yada Labarai na Mataimakin Gwamnan Jihar Yobe ya fitar a ranar Talata ta ce “sun sauya sheka ne saboda kyakkyawan jagoranci jam’iyyar APC a karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ”.

Sanarwar ta kuma nakalto Mataimakin Gwamnan Yobe, Alhaji Idi Gubana yana “tabbatar wa sabbin masu shigowa da adalci kuma za’ayi tafiya da su tare don kai jam’iyyar zuwa babban matsayi”.

Gubana ya kuma ce gwamnan yana da ikon tafiya da kowa da kowa, ba tare da la’akari da banbancin siyasa ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *