fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Yanzu-Yanzu:Boko Haram sun kashe Kwamandan Sojoji da wasu sauran sojoji 13 a Borno

Rahotanni daga Mainok dake jihar Borno na cewa, Kungiyar Boko Haram ta kashe Kwamandan Sojoji me mukamin Lieutenant Colonel a harin data kaiwa garin da yammacin yau.

 

Hakanan Wata majiyar Soji ta bayyanawa The Cable cewa Boko Haram din sun kuma kashe sojoji 13.

 

Sun shiga garinne da misalin karfe 2 na rana inda suka yi basaja a matsayin tawagar Sojoji, suka samu shiga sansanin sojin. Saida suka raba tsaka, sannan suka budewa Sojojin wuta.

 

Rahoton yace bayan korar Sojojin daga barikin, sun kwashe makamansu. Majiyar ta kara da cewa Jirgin yaki ya zo yayi ruwan bamabamai amma saidai be samu Boko Haram din ba wanda hakan yasa suka ci gaba da aika-aikar da suke.

 

Bayan sansanin Sojin, Boko Haram sun kuma kona Ofishin ‘yansanda na garin, hakanan majiya r tace sun kwashe awanni 2 a garin kamin daga baya su fice.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *