fbpx
Monday, October 25
Shadow

Yanzunnan: An gano wasu ‘yan majalisa 2 da ake zargi da hannu a ayyukan ‘yan Bindiga

Majalisar jihar Zamfara ta dakatar da wasu ‘yan majalisar 2 saboda zargin suna da hannu a ayyukan ‘yan Bindiga.

 

‘Yan majalisar da aka dakatar sune, Yusuf Anka sai kuma Ibrahim T. Tukur Bakura.

 

Daily Trust ta ruwaito cewa an dakatar dasu ne na tsawon watanni 3.

 

Daraktan Yada labarai na majalisar, Mustapha Jafaru Kaura ya tabbatarwa da majiyar dakatarwar inda yace sai an kammala bincike tukuna za’a san matsayin ‘yan majalisar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *