fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Yanzunnan: Gwamnatin tarayya ta amince ta biya bukatun Likitoci

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, ta amince ta biya bukatun Likitocin dake yajin aiki.

 

Saidai tace ba zata ci gaba da biyansu Albashi ba sai sun koma bakin aiki.

 

Likitocin sun kwashe kusan wata daya suna yajin aiki inda har kotun ma’aikata ta ce su koma amma suka ki.

 

Hakanan majalisar tarayya ta so shiga tsakani kan lamarin amma abin ya faskara.

 

Ministan kwadago, Chris Ngige ne ya bayyana amincewa da biyan bukatun likitocin bayan ganawa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *