fbpx
Monday, September 27
Shadow

Yanzunnan: Mayakan Boko Haram sama da 400 da akawa horo a kasashen Libya da Mali sun dawo Najeriya

Rahotanni na cewa, mayakan Boko Haram sama da 400 da akawa horo a kasashen Libya da Mali sun dawo Najeriya.

 

Mayakan sun shigo Najeriya ne ta kasar Nijar kamar yanda kafara dake kawo labaran tsaro, EONSINTELLIGENCE ta ruwaito.

 

Boko Haram ta dawo da mayakan ne wanda kungiyar ISIS tawa horo saboda yawan mayakanta da ke tuba suna mika wuya ga sojojin Najeriya.

 

A watan Mayu da ya gabata, mayakan Kungiyar ISWAP data balle daga Boko Haram 300 ne da akawa Horo a kasashen waje suka jagoranci yakin da yayi sanadiyyar mutuwar shugaban Boko Haram,  Abubakar Shekau.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *