fbpx
Wednesday, January 26
Shadow

Yanzunnan:Ma’aikatan shugaba Buhari sun kamu da coronavirus

Rahotanni dake fitowa daga fadar shugaban kasa na cewa, ma’aikatan shugaban kasa, Muhammadu Buhari sun kamu da cutar coronavirus.

 

Dalilin hakan, sun killace kawunansu kamar yanda doka ta tanadar.

 

Wadanda suka kamu din sune Tijjani Umar wanda babban Sakatare ne a fadar shugaban kasar, sai kuma dogarin shugaban kasar, watau Yusuf Dodo, sai kuma kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu, kamar yanda Premium times ta ruwaito.

 

Rahoton yace hakanan shima ministan yada labarai, Lai Muhammad ya kamu da cutar.

 

Saidai cutar bata musu illa sosai ba saboda duk sun yi rigakafi

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *