fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Yanzunnan:’Yan Bindiga sun kaiwa Sojojin Najeriya harin kwantan bauna sun kashe wasu, wasu sun jikkata

Rahotanni daga jihar Naija na cewa Sojojin dake kan hanyar kubutar da wasu ds aka sace sun afkawa harin kwantan bauna na ‘yan Bindiga.

 

An kashe sojojin 2, wasu da dama sun jikkata a harin.

 

Sojoji 13 ne ake duba lafiyarsu a Asibitin dake Minna yayin da wasu kuma da suka jikkata sosai an wuce dasu Kaduna.

 

Daya daga cikin sojojin da ya jikkata, Major D. Omale ya bayyanawa gwamnan Naija, Abubakar Sani Bello da ya kai musu ziyara cewa, ‘yan Bindigar su kusan 200 suka afka musu.

 

Jimullar sojoji 18 ne suka jikkata a harin kamar yanda Sunnews ta ruwaito.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *