fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

‘Yar Asalin Jihar Katsina Ta Kafa Tarihin kammala Digiri da First Class daga jami’ar Nile

Matashiya Hajara Kabeer Abdulfatah, Yar Asalin Jihar Katsina Da Ta Kammala Digirinta A Jami’ar Nile Dake Abuja, Da Sakamako Mafi Kyau Watau First Class A Bangaren Harkar Injiniyar Man Fetur Da Iskan Gas.

Zakakurar Dalibar Ta Samu Nasarar Rubuta Makalar A Bangaren Da Ta Kware, Wadda Rubutun Nata Ya Sanya Ta Yi Zarra Ga Abokan Karawarta, Inda Ta Wakilci Kafatanin Kasashen Afirika A Garin Dallas Na Jihar Texas A Kasar Amurka.

Ta Taba Zama Shugabar Dalibai Masu Karantar Injiniyar Man Fetur Da Iskan Gas Ta Najeriya A Jami’ar Nile Dake Abuja. An Kuma Karramata Da Kyautuka Daban-daban. Ta Je Sanin Makamar Aiki A Hukumar Kula Da Albarkatun Man Fetur Da Kuma Kamfanin Makamashi Na Oriental.

Rariya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *