fbpx
Thursday, August 5
Shadow

‘Yar shekaru 13 ta kashe kanta saboda faduwa jarabawa

Yarinyar ‘yar kasar Uganda ta kashe kanta ne bayan faduwa jarabawar sannan kuma iyayenta suka mata fada.

 

Yarinyar me suna Daphine Nikimuli ta kashe kanta sannan kuma ta bar wasika kan dalilin da yasa ta aikata hakan.

 

Yarinyar taci 28 cikin makin gaba daya jarabawar. Ta bayyana a cikin wasikarta yanda ‘yan uwa da iyayenta ke ta hantararta saboda sakamakon jarabawar.

Yarinyar tace an nuna mata ba’a sonta, dan haka ta fita bayan gidansu ta kashe kanta. ‘Yansanda sun ce tuni suka fara bincike kan lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *