fbpx
Monday, November 29
Shadow

Yaren Hausa ya samu babban matsayi a kasar Saudiyya

Hukumomin da ke kula da Masallatai Biyu Masu Daraja na Saudiyya sun ƙaddamar da wani shiri na yin fassara da jagoranci ga masu aikin Umrah a Masallacin Ka’aba da na Annabi SAW a Madina zuwa harsuna bakwai.

Za a ajiye masu fassara a masallatan ga duk wani mai neman sani kan batutuwan da suka shafi addinin Islama da kuma ayyukan ibadah a masallatan.

Harsunan sun ƙunshi Inglishi da Urdu da Farisanci da Faransanci da Hausa da Bengali da kuma harshen Turkiyya.

Mahajjata da masu Umrah da masu ziyara za su samu amsoshin tambayoyinsu da harshen da suke so ciki har da Hausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *