fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Yarinyar da ta taba haihuwa tana da shekaru 13, ta sake daukar ciki

Wata yarinya data dauki ciki tana da shekaru 13 a shekarar 2020, ta sake daukar wani cikin.

 

Darya Sudnishnikoblva ‘yar kasar Rasha a shekarar data gabata, ta bayyana cewa, saurayinta me shekaru 10 ne ya mata cikin.

 

Saidai daga baya, ta bayyana cewa, wani dan shekaru 14 ya mata fyade. A karshe dai ta haifi diyarta, a watan Augusta na shekarar 2020.

 

Yarinyar ta bayyana cewa, a yanzu, wani dan shekaru 17 ne kuma ya dirka mata cikin. Ta kara da cewa amma ya musanta cewa shine ya mata cikin.

 

Tace gaskiya ba zata iya sake haihuwa ba, saboda ta gane da wuya ta iya rainon wani da a yanzu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *