fbpx
Monday, September 27
Shadow

Yaro dan shekara biyar ya rasa ranshi sakamakon fadawa rijiyar a jihar Kano

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani yaro dan shekara biyar, Yusha’u Usman, bayan ya fada cikin rijiya a Zangon Dinya a karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Saminu Abdullahi, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Juma’a a Kano.

Abdullahi ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren Alhamis.

“Mun samu kiran gaggawa daga bangaren Bichi da misalin karfe 08:30 na dare. daga wani mutum mai suna Muhammad Usman kuma mun aika da jami’an mu na ceto zuwa wurin da karfe 08.45 na yamma, ”inji shi.

Abdullahi ya ce, an fito da Usman daga cikin rijiya matacce.

Ya ce ana gudanar da bincike kan lamarin.

Abdullahi ya kara da cewa an mika gawar yaron da ya nutse a hannun hakimin Zangon Dinya Bagwai, Malam Yahaya Sule.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *