fbpx
Monday, September 27
Shadow

Yaudarar mu kawai kuke>>ASUU ta gayawa Gwamnatin tarayya

Kungiyar malaman jami’a ta ASUU reshen jihar Kano ta bayyanawa gwamnatin tarayya cewa yaudararsu take.

Ta bayyana hakane saboda kin cika alkawuran da gwamnatin tarayyar ta dauka a shekarar data gabata.

Shugaban ASUU reshen jihar, Professor Abdulkadir Muhammad ne ya bayyana haka inda yace, akwai Biliyan 30 wadda tana daga cikin Biliyan 220 da gwamnatin tace zata bayar ta gyaran jami’o’in.

Ya kara da cewa akwai kuma Biliyan 25 da gwamnatin tawa jami’o’in Alkawari amma har yanzu babu wanda aka cika.

Yayi kiran cewa, suna fatan gwamnatoci zasu kawowa makarantun dauki dan a samu ci gaban da ya dace.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *