fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Yawan wanda suka mutu a fafatawar Zirin Gaza tsakanin Yahudawan Isra’ila da Falasdinawa sun kai 70, da yara 16, Amma Isra’ila tace ba’a ga komai ba, yanzu ta fara

Kasar Isra’ila ta bayyana cewa ruwan bamabamai da takewa Falasdinawa a zirin Gaza, yanzu ta fara, dan kuwa ba’a ga komai ba.

 

Hakan na zuwane yayin da Mailonline ta ruwaito cewa, yawan wanda suka mutu a hare-haren sun kai 70 wanda akwai kuma yara kanana 16.

 

Shugaban Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa, Falasdinawa zasu ga gagarumin tashin hankalin da basu taba mafarkinsa ba.

 

Isra’ila ta yi ikirarin kashe manyan Shuwagabannin kungiyar Hamas guda 11. Kowane bangare na Asara amma an fi yiwa Falasdinawa. Wasu rahitannin sun ce an kashe sama da falasfinawa 60 yayin aka kashe Isra’ilawa 7.

 

Saidai duk da wannan ruwan bamabamai da Isra’ila kewa Falasdinawa,  kungiyar Hamas har yanzu bata daina cilla mata rokoki ba, a baya Isra’ila ta koka da cewa, Hamas na jefa mata Roka 1 a duk cikin mintuna 3, inda wani rahoton kuma yace, Hamas ta cilla jimullar Rokoci 1500 cikin Isra’ila.

 

Kalli bidiyon irin ruwan bamabamai da Hamas kewa Isra’ila a kasa:

 

Wannan Sojan Yahudawan Isra’ila ne da aka kashe.

 

Wadannan hotunan wasu Falasdinawa ne da aka kashe.

Duk da Isra’ila na da abinda ke tare Rokokin, Amma Lamarin na neman gagararta inda wasu daga cikin rokokin na fadawa kasarta suna mata illa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *