fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Yawan Yaran da basa zuwa Makaranta a Arewa Abin tashin Hankaline>>A’isha Buhari

Uwargidann shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari ta bayyana damuwa da yawan yaran da basa zuwa makaranta da ake dasu a Arewa inda tace lamarin na bukatar kulawar gwamnati da gaggawa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

A’isha Buhari ta bayyana hakane a jihar Adamawa lokacin da take kaddamar da shirin ta na baiwa matasa 750 horo a jihar karkashin kungiyar ta ta tallafawa mata da matasa me suna Future Assured.

A’isha Buhari ta bakin wakilinta a wajan taron kuma mataimakin shugaban makarantar Jami’ar ABTI, Dr. Abba Tahir ta bayyana cewa abubuwa irin su al-ada da matsalar ‘yan tada kayar baya da kuma rashin karfafawa malaman makarantar duk sun tallafa wajan rashin halartar yaran zuwa Makaranta musamman ma yara mata.

Tace kuma ba za’a yi watsi dasu dan haka lamarin ke bukatar kulawa ta gaggawa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *