fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Yayin da ake rade-radin mutuwar aurensu: Mansurah Isah ta saka hoton iyalinta tare da Sani Danja

Tsohuwar Tauraruwar fina-finan Hausa, Mansurah Isah ta saka hoton iyalanta a shafinta na Instagram inda ta cewa masoyanta, suna musu gaisuwar Sallah.

 

Hakan na zuwane yayin da a baya aka rika rade-radin cewa, auren Mansurah Isah da Sani Danja ya mutu.

 

Tun bayan wancan lokaci dai da aka rika yada wancan labarin, ba’a ji ta bakin ma’auratan ba. Amma Mujallar Fim tace ta samu daga majiya me karfi cewa, Mansurah Isah ta kama gida kusa da gidan Sani Musa Danja.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *