fbpx
Saturday, April 17
Shadow

Yayin da Gwamna Wike ya bayar da Miliyan 500 a Sokoto, Kungiyar gwamnonin APC ta ba da gudummawar Naira miliyan 50 ga Zamfara kan gobarar kasuwar Tudun Wada

Kungiyar gwamnonin APC ta ba da gudummawar Naira miliyan 50 ga gwamnatin jihar Zamfara don taimakawa wajen sake gina kasuwar Tudun Wada da gobara ta lakume a makon da ya gabata.
Tawagar wanda shugabanta, Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya jagoranta ya bayar da gudummawar kudin a gidan gwamnati da ke Gusau, yana mai cewa an yi hakan ne ba tare da la’akari da cewa Zamfara a yanzu jihar PDP ce ba.
Gwamna Bagudu ya lura cewa taron ya zo jihar Zamfara ne daga Katsina inda suka ziyarta sun duba wata gobarar da ta faru kwanan nan wacce kuma ta cinye kasuwa.
A nasa martanin, Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya nuna shakku kan karimcin yana mai cewa bai tabbata ba ko kyautar ta kasance wata dabara ce da Gwamnonin APC ke yi don jawo shi zuwa cikin kungiyar su.
“Duk da haka ina yabawa APC saboda ni ba dan jam’iyyar APC bane amma sun kawo min ziyarar hadin kai ni da jiha ta da kudi naira miliyan 50”
“Kamar yadda nake magana da ku, babu wata jam’iyyar PDP da ta ziyarci Zamfara tun lokacin da wutar ta tashi a kasuwar Tudun Wada a makon da ya gabata”
Matawalle ya ce tunda Gwamnonin APC suka kawo Naira miliyan 50 din zuwa Jihar Zamfara, ba za a iya maida su ba.
Rahoto ya ce tawagar a ziyarar sun hada da Gwamnonin Jihohin Kebbi da Jigawa da kuma Shugaban riko na Jam’iyyar APC, Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai Mall a Buni.
A baya dai Gwamna Wike ya bayar da tallafin Miliyan 500 ga jihar Sokoto da gobara ta tashi a kasuwa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *