fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Yayin da Gwamnoni ke ta korafin Shugaba Buhari ne ke da alhakin samar da tsaro, Gwamnan Kogi yace, baya bukatar Shugaba Buhari kamin ya samar da tsaro a jiharsa

Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello ya bayyana jiharsa a matsayin jiha da ta fi kowace jiha zaman Lafiya a Najeriya.

 

Ya bayyana hakane a wajan taron bikin cikarsa shekaru 46 a Duniya. Gwamnan yace a lokacin da ya karbi mulkin jihar Kogi, Suna fama da matsalolin tsaro da suka fi wanda ake fama dasu a Najeriya a yanzu.

 

Yace amma kasancewar ya shawo kan matsalar,  yanzu Kogi ta samu zaman lafiya, suna kallon junansu a matsayin ‘yan kasa ba tare da nuna banbancin Addini ko Kabila ba.

 

Gwamnan yace baya jiran shugaban kasa kamain ya samar da tsaro, baya bari lamarin ya sha karfinsa har ta kai ga yanda shugaban kasa zai shigo.

 

Ya kuma kara da cewa, mutum zai iya yawo ko ina a cikin jihar Kogi ba tare da matsala ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *