Sanata mai wakiltar Borno ta kudu, Ali Ndume ya bayyana cewa yin afuwa ga ‘yan fashi kamar yadda shahararren malamin addinin Islama Sheikh Gumi ya ba da shawara na iya haifar da sabon salo na aikata laifuka.
Ndume ya bayyana hakan ne a cikin wani shirin na gidan talabijin a ranar Lahadi 28 ga Fabrairu.
Ndume wanda ya ce dole ne gwamnati ta magance matsalar ‘yan ta’addan ta hanyar amfani da jami’an tsaro, kuma tayi watsi da shawarar yin afuwa ga’ yan ta’addan domin hakan na iya ƙarfafa sauran kungiyoyin masu aikata laifuka.