fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Za mu amince da kasafin kudin baɗi kafin karshen 2021

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Lawan ya ce majalisar dokoki za ta amince da kasafin kudin 2022 kafin karshen wannan shekarar.

Lawan ya bayyana haka ne a jawabinsa na maraba kafin shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2022 a zauren majalisar dokokin kasar.

Bayan godewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, shugaban majalisar dattawan ya ce ‘yan majalisar za su yi aiki tukuru domin ganin an soma aiki da sabon kasafin kudin a cikin sabuwar shekara.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *