fbpx
Sunday, September 26
Shadow

Za mu ci gaba da ciwo bashi – APC ta fada wa PDP

Jam’iyyar APC mai mulkin kasar ta yi kakkausar suka ga Jami’iyyar PDP kan yadda Shugaba Muhammadu Buhari yake ciyo bashin, inda ta ce yana yi ne don amfanin kasar ne.

Jam’iyyar ta ce kudaden da aka aro “ana amfani da su ne don bunkasa muhimman ababen more rayuwa wadanda ke karfafa ci gaban tattalin arziki, samar da ayyukan yi, rage talauci da inganta jin dadin jama’a baki daya.”

Sakataren Kwamitin Tsare-Tsaren Babban Taron Jam’iyyar APC (CECPC) Sanata John James Akpanudoedehe, a martanin da jam’iyyar adawa ta PDP ta yi game da kudirin da Gwamnatin Tarayya ta gabatar, ya ce basussuka a karkashin gwamnatin da APC ke jagoranta suna da fa’ida kuma a zahiri ana yi amfani da su ta hanyar da ya dace ba irin lokacin PDP da ake ciyo bashi don amfanin wasu daidaikun mutane.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *