fbpx
Monday, May 10
Shadow

Za mu tsige Buhari idan rashin tsaro ya ci gaba>>Dan majalisa, Bagos

Wani dan majalisa mai wakiltar Mazabar Tarayyar Jos ta Kudu da Jos ta Gabas a Majalisar Wakilai, Dachung Bagos ya ce Majalisar Tarayya za ta duba yiwuwar tsige Shugaban Kasa Muhammadu Buhari idan har bangaren zartarwa bai yi aiki da kudurin ta na tsaro ba.
Dan majalisar ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake bayyana a shirin talabijin na Channels Sunrise Daily.
Ku tuna cewa majalisar wakilai a ranar Laraba ta kaddamar da kwamiti na mutum 40 don nemo mafita ga kalubalen tsaro na kasar.
Kwamitin zai shirya taron kwanaki hudu na tsaro a watan Mayu.
Bagos yayin shirin TV ya ce za a fara aiwatar da tsigewar idan ba a zartar da kudurorin taron ba ta bangaren zartarwa bayan wasu watanni.
“Idan har babu abin da bangaren zartarwa ke yi bayan wannan karshe to muna kira da a tsige shugaban.
“Muna da ikon tsige shugaban kasar idan har ba zai iya ci gaba da tsare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya ba”, in ji shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *