fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Za’a fara tura matasa masu Hidimar Kasa zuwa kasashen waje

Hukumar kula da masu hidimar kasa ta NYSC na duba yiyuwar fara aika dalibai masu hidimar kasar zuwa kasashe 16 dake karkashin kungiyar ECOWAS ta Africa ta yamma.

 

Farfesa Oko Obono na jami’ar Ibadan ne ya bayar da wannan shawara a wajan wani taro da aka yi a Suleja.

 

Ya bada Shawara cewa kai daliban kasashen yammacin Africa za rage yawan marasa aikin yi da kuma budewa dalihan ido kan yanda Duniya take da kuma sada zumunta tsakanin kasasbe.

 

Shugaban NYSC, Janar Shuaibu Ibrahim ya bayyana cewa, zaau duba wannan shawara dan ganin ko zai yiyu a fara amfani da ita.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *