fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Za’a wa shugaba Buhari Zanga-Zangar kiyayya a Birnin New York

Wata kungiyar masu fafuukar neman ‘yancin kai ta ‘yan Najerya mai lakabin NINAS, ta ce babu gudu ba ja da baya, kan shirinta na yin zanga-zanga a shalkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York, yayin da shugaban kasar Muhammadu Buhari zai gabatar da jawabinsa ga jama’ar duniya a ranar Juma’ar nan.

Cikin wata sanarwa da daraktan watsa labaran kungiyar Maxwell Adeleye ya aike wa jaridar The Nations ta Najeriya, ya zargi gwamnatin shugaba Muhamadu Buhari da daukar nauyin wata zanga-zanga a lokacn don yi wa ta su makarkashiya.

Ya yi zargin cewa gwamnatin na hayar bakake ‘yan Amurka domin su saje a matsayin ‘yan Najeriya don nuna cewa suna tare da shugaba Buhari.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *