fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Zaben Kaduna: PDP ta lashe kujerar Shugabancin karamar hukumar Jaba

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kaduna ta ayyana Mista Phillip Gwada, PDP, a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar shugabancin karamar hukumar Jaba a zaben da ya gudana a ranar Asabar.

Jami’in zaben, Farfesa Peter Omale, ya bayyana hakan a ranar Litinin a ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar, SIEC, a Kwoi.

Mista Omale ya ce Gwada ya samu kuri’u 9,012 inda ya kayar da dan takarar APC, Mista Benjamin Jock, wanda ya samu kuri’u 5,640.

Ya ce dan takarar Action Democratic Party, Alhamdu Gyet, ya zo na uku da kuri’u 2,732.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *