fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Zambia ba za ta amince da ayyukan luwaɗi ba>>in ji shugaban ƙasar

Shugaban Zambia Hakainde Hichilema ya ce ƙasarsa ba za ta amince da ayyukan luwaɗi ba saboda kasace taaddinin Kirista.

Shugaba Hichilema ya ce ƙasar za ta iya”tafiya da kyawawan dabi’u na demokradiyya da sauran ƙasashe”, kamar yadda kafofin yaɗa labarai na cikin gida suka ruwaito.

A watan da ya gabata, shugaban ya musanta yin tattaunawa kan batun ƴancin ƴan luwaɗi da maɗigo a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya a Amurka.

Tun da farko wasu kafofin yaɗa labarai na ƙasar sun ce an soke ganawar da aka shirya yi tsakanin shugaba Hichilema da shugaba Joe Biden sakamakon kalaman ƙyamar luwaɗi da mataimakin shugaban Zambia Mutale Nalumango ya yi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *