fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Zamu bayar da bashi amma bana bati bane sai kun biya>>Gwamnatin Tarayya

Ministan ma’adanai, Olamilekan Adegbite ya bayyana cewa, sun warw Miliyan 200 dan tallafawa kananan masu hakar ma’adanai.

 

Ya bayyana hakane a wajan wani taro ranar Talata. Yace akwai Biliyan 3.2 da aka baiwa bankin masana’antu ya rabawa ‘yan Najeriya amma saboda tsauraran matakan da aka sakawa karbar bashin, yanawa kananan masu hakar ma’adanai wahalar karba.

 

Yace dan hakane suka ware wannan Miliyan 200 dan kananan masu hakar ma’adanai. Yace mafi karancin bashin da za’a baiwa mutum shine 200,000 zai kuma Miliyan 2 a matsayin mafi yawan bashin.

 

Yace abinda kawai ake bukata shine mutum ya kawo wanda zai tsaya masa dake matsayi na 14 na Albashi a aiki.

 

Yace amma fa wannan kudi bana bati bane, za’a biya akan ruwa na kaso 5 cikin 100.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *