fbpx
Saturday, June 19
Shadow

Zamu ci gaba da baki goyon baya har ki yi nazarar zama shugabar WTO>>Shugaba Buhari ga Ngozi

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya baiwa tsohuwar ministar kudi, Ngozi Okonjo Iwaela tabbacin zai ci gaba da bata goyon bayan ganin ta zama shugabar cibiyar Kasuwanci ta Duniya.

 

An dai ta gurzawa da Ngozi har ta zama yanzu su biyu ne suka rage wanda za’a dauki daya daka cikinsu ta zama shugabar WTO.

Shugaban kasar ya baiwa Ngozi wannan tabbaci ne a yayin ziyarar da ta kai masa jiya a fadarshi dake Abuja.

 

Hadimin shugaba Buhari,  Bashir Ahmad yace shugaban ya bayyana cewa zasu yi dukkan mai yiyuwa wajan ganin cewa Ngozi ta samu wannan mukami, ba wai dan kawai ta na ‘yar Najeeiya ba sai dan ta cancanta.

“I assure you that we will do all that we can to ensure that you emerge as the Director-General of WTO, not only because you are a Nigerian, but because you are a hardworking Nigerian. You deserve this.”, President @MBuhari assures @NOIweala, Nigeria’s candidate for the DG WTO.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *