fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Zamu gina gidajen da Ambaliyar ruwa ba zata musu komai ba>>Kasar Amurka

Shugaba Joe Biden ya yaba da yadda aka tunkari barnar da mahaukaciyar guguwa da ruwa da aka wa lakabi da Ida ta yi a Louisiana and Mississippi a ranar Lahadin da ta wuce.

Shugaban ya yi alakawrin taimaka wa mutane sake gina garuruwansu da kayan da za su iya jure wa irin wannan mahaukaciyar guguwa da ruwa.

A yayin ziyarar da ya kai garin LaPlace (LaPlas), yamma da New Orleans, Mista Biden ya ce, gwamnatinsa za ta tabbatar kamfanonin inshore masu zaman kansu sun biya jama’a wadanda suka tsere wa bala’in daga gidajensu asarar da suka yi.

Shugaba Biden ya jajanta tare da tabbatar wa da jama’a a Louisiana cewa gwamnatin tarayyar tana tare da su.

A ziyarar da ya kai, yana dubawa ya gane wa idonsa irin illar da bala’in ya haifar, shugaban ya ga irin bacin ran da jama’a da yawa suka nuna, kan jinkirin da aka samu na mayar musu da wutar lantarki.

Ya gaya musu cewa an aika da ma’aikata dubu 25 domin su gaggauta gyara matsalar wutar lantarkin. Wasu garuruwa da unguwannin tsawon kwanaki ba su da lantarki da ruwan famfo da kuma abinci.

Mista Biden ya ce ana ware dala mliyan dari daya ta taimako, inda za a ba kowa ne mutum dala dari biyar domin sayen kayan da yake bukata na gaggawa.

Ya ce idan aka tashi sake gina muhimman kayayyakin jin dadin jama’a da ruwa da guguwar suka lalata, to za a gina su ne ta yadda, wata mahaukaciyar guguwa da ruwa a nan ga ba za su iya lalata su ba.

Ya ce : ”Abubuwa na sauyawa da sauri da sauri, a game da muhalli. Tuni mun tsallake wani mataki, ba za mu iya gina titi, babbar hanya, gada ko wani abu kamar yadda yake a bay aba. Wato dole ne ka gina abu kamar yadda ya kamata ya zama a yanzu, yadda ake bukatarsa a yanzu.”

Ya kara da cewa balai’in ya nuna muhimmancin inganta tsarin samar da makamashi (lantarki) da kuma gine-gine masu karfi da za su iya jure mahaukaciyar guguwa mai ruwa.

Can a New York ma inda bala’in na guguwar ta Ida ta yi wa barna, jami’ai sun yi gargadin cewa akwai bukatar a inganta abubuwa, kamar magudanun ruwa da suka fi na yanzu da kuma yadda za a kare hanyoyin karkashin kasa na jirgin kasa, saboda za a rika samun ambaliyar ruwa a kai a kai, saboda sauyin yanayi.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *