fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Zanga-zanga ta barke a Jihar Oyo yayin da jami’an kwastan suka kashe mutane biyar a lokacin da suke musayar wuta da wasu yan fasa kwauri

Anyi hatsaniya a garin Iseyin, jihar Oyo, a ranar Alhamis, yayin da wasu jami’an hukumar kwastam ta Najeriya suka kashe mutane biyar a garin yayin artabu da wasu da ake zargin masu fasa-kwaurin ne.

An ce mutanen Kwastam din na bin motar Utility Vehicle dauke da shinkafa a lokacin da rikicin ya barke.

Mazauna yankin sun shaida wa manema cewa jami’an Kwastam din sun fara harbi kuma harsasai suka fada kan wasu mutane, wadanda ke wajen bikin Eid-il-Fitri, kuma biyar daga cikinsu sun mutu.

Wannan kashe-kashen ya haifar da gagarumar zanga-zanga a garin.

An yi ikirarin cewa matasa masu zanga-zangar sun kone sansanin na Hukumar kwastan da ke garin, tare da kone wasu motoci.

A kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ta kwastan, ta hanyar mai kula da shiyyar Oyo / Osun, Mista Kayode Wey, amma daga bisani abin ya ci tura, an kira wayarsa a kashe.

Amma, Aseyin na Iseyin, Oba Abdulganiyy Salau, ya yi Allah wadai da kisan a cikin wata sanarwa.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *