fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Zanyi maganin yan bindinga da suka ki tuba – Gwamna Bello Matawalle

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bayyana shirye-shiryen sauya dabarun yaki da ‘yan bindiga da ba su tuba ba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da yake karbar bakuncin Gwamna Atiku Bagudu na Kebbi da Abubakar Badaru na Jigawa wadanda suka je jihar don yi masa jajen kan hare-haren ‘yan bindiga a jihar.

Babban Daraktan gwamnan kan harkokin yada labarai, wayar da kan jama’a da sadarwa, Idris Idris-Gusau, a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, yace Gwamna Matawalle a cikin kwanaki hudu masu zuwa, ya sha alwashin ganin bayan duk masu aikata laifuka a fadin jihar.

Ya kara da cewa, yan bindingar da suka ki tuba su kuka da kansu domin kuwa Gwamnati ta shirya kawar su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *