fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Zinedine Zidane ya canja ra’ayi, watakila a yanzu ya karbi aikin horar da Manchester United

Rahotanni sun bayyana cewa, Zinedine zidane ka iya canja ra’ayi ya karbi aikin horas da kungiyar Manchester United.

 

A baya dai da aka masa tayi, Zidane ya ce a kai kasuwa ba zai yi ba, kamar yanda wasu majiyoyi suka ruwaito.

 

Saidai daga baya, Manchester United ta dukufa wajan ganin ko ta halin kaka ta kawo Zidane ya horar da ‘yan wasanta.

 

Hakana  Rahotanni sun nuna cewa ana samun ci gaba a kokarin na Manchester United ta kawo shi ya mata aiki.

 

Saidai duk da haka a yanzu Ole Gunnar solskjær ya koma aikin horas da ‘yan wasan na Manchester United ranar Talata bayan hutun da aka tafi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *