fbpx
Thursday, April 22
Shadow

Zuwan Coronavirus/COVID-19 ya nuna mana cewa shugaba Buhari zai iya zama ba tare da tafiye-tafiye ba>>PDP

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya shafe watanni 8 ba tare da ya fita kasar wajw ba, wannan ne lokaci mafi tsawo da ya zauna a Najeriya ba tare da yin tafiye-tafiye ba cikin shekaru 7 da ya kwashe yana mulki.

 

Zuwan cutar Coronavirus/COVID-19 ya taimaka sosai wajan hana shugaban kasar tafiye-tafiye saboda kasashen Duniya sun saka dokar hana shiga kasashen su sannan kuma cutat ta kashe sama da mutane Miliyan 2 ciki hadda tsohon shugaban ma’aikatan shugaban kasar, Malam Abba Kyari.

 

Amma duk da haka a cikin kasafin kudin shekarar 2021 an ware Biliyan 1.751 a matsayin kudin tafiye-tafiyen da shugaban kasar zai yi zuwa kasashen waje yayin da aka kuma ware Miliyan 775.6 a matsayin kudin tafiye-tafiyen da shugaban kasar zai yi a cikin Najeriya.

 

Jam’iyyar PDP da take sukar shugaban kasar tace ashe dai zai iya zama a Najeriya ba tare da tafiye-tafiye ba, sannan kuma ta nemi a dawowa da Najeriya kudaden da aka ware na tafiye-tafiyen nasa tunda bai yi su ba.

 

A baya dai, hutudole.com ya ruwaito muku yanda aka yi taron tunawa da marigayi, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto a Kaduna.

 

Also, the Peoples Democratic Party asked Buhari to disclose to Nigerians the amount of unspent funds for travelling and return them to the federal purse, adding that the President must tell Nigerians what the country has gained from his stay at home over the past eight months without an official trip outside the country.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *