Pages

Wednesday 10 January 2024

Amfanin tafarnuwa ga azzakari dan jin dadin jima'i

Amfanin tafarnuwa ga azzakari:

Ga maza masu fama da matsalar rashin karfin mazakuta, Tafarnuwa na taimakawa wajan magance wannan matsala.

 

Hanya ta farko da ake amfani da tafarnuwa wajan magamce matsalar rashin karfin mazakuta ko kuma kara karfin jin dadin jima'ai shine a saka tafarnuwar a cikin abinci ko kuma a shayi a sha.

 

Hakanan idan ana fama da matsalar rashin karfin mazakuta, ana iya cin tafarnuwa 3 kullun.

 

Aci har zuwa tsawon wata 3 dan samun sakamako me kyau.

 

Ana kuma hada tafarnuwa da Zuma ko Madara:

Hakanan namiji me neman karin karfin mazakuta, yana iya yin hadin tafarnuwa da madara ko kuma zuma dan samun karfin gaba.

 

Zaka samu Tafarnuwa kamar balli biyu ka murzata sai ka hada da zuma ko madara kasha.

 

A sha wannan hadi da safe kamin fara cin abinci har na tsawon watanni 3 zuwa 4.

Amfanin Tafarnuwa ga Namiji:

Tafarnuwa na da matukar amfani ga namiji wajan kara karfin mazakuta da kuma kara jin dadin jima'i.

 

Wasu ba zasu so cin tafarnuwa kai tsaye ba dan haka ana iya sakata a dafa a abinci ko a hada da wani abin da ake son ci, irin su burodi, nama ko sauransu.

Illar Tafarnuwa:

Wasu na samun matsala yayin da suka yi amfani da tafarnuwa.

Matsalolin sun hada da numfashi sama-sama, kumburin fuska, Lebe da Harshe, da kaikayin Makogoro.

Wasu ma kan yi habo, ko kuma zubar jini ta baki da sauransu.

Idan an ji irin wannan a dakata da amfani da tafarnuwa a tuntubi likita.

Hakanan akwai matsalar warin baki da warin jiki, ciwon kirji, amai ko zawo da masu cin tafarnuwa kan yi fama dasu.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment