Pages

Tuesday 2 January 2024

yadda ake gwajin ciki da gishiri



Daya daaga cikin hanyoyin da ake gwajin ciki na gargajiya shine ta hanyar amfani da gishiri.

 

Ya da zaki yi shine, ki samu gishiri kamar cokali daya sannan ki samu fitsarinki shima kamar cokali daya.

 

Sai ki samu kofi ko kwano ki zuba su duka a ciki.

 

Ki basu kamar minti 15 haka, idan gishin ya bace to baki da ciki, idan kuma yayi gudaji-gudaji ko kumfa to kina da ciki.

 

Menene ingancin wannan gwajin?

A likitance dai ba'a tabbatar da ingancin wannan gwajin ba amma da yawa suna amfani dashi wajan gano cewa suna ciki ko babu.

 

A wajan wasu yana aiki a wajan wasu baya yi.

 

Akwai hanyoyi da yawa na gwajin ciki na gargajiya, danna nan domin karantasu.


 Hanya mafi inganci da zaki gane kina da ciki ko babu shine daukar hoto ko kuma aje a yi gwaji

No comments:

Post a Comment