Pages

Tuesday 18 October 2016

Rigar da A'isha Buhari ta saka zuwa kasar Belgium ta jawo cece kuce

A yaune uwargidan shugaban kasa A'isha Buhari taje can kasar Belgium Birnin Brussels inda zata halarci wani taron wanda za'a tattauna matsayin mata a harkar tsaron duniya, rigar data saka wajen yin tafiyat ta fara jawo cece kuce a shafukan sada zumunta na yanar gizo bayan da aka gano cewa kudin rigar sunkai dalar amurka $2,600 dubu biyu da dari shida. Wanda idan aka juya kudin zuwa naira rigar zata tashi akan naira miliyan daya da dubu dari biyu N 1,200,000.



Wasu na ganin cewa be kamata a ganta da riga me tsada irin wannan ba a lokacin da Najeriya ke cikin matsin tattalin arziki, amma wasu na ganin saka rigar ba komai bane tunda itace matar shugaban kasa.


No comments:

Post a Comment