Pages

Saturday 12 August 2017

"Kyautar 'yan siyasa ta neman kuri'ace, shahararrun mutane suke kyauta tsakani da Allah">>General BMB

Jarumin fim din hausa, Bello Muhammad Bello(General BMB), ya saka wannan hoton da aka hada hotuna guda hudu a cikinshi, na farko hoton tsohon shugaban kasane, Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar yana cin abinci tare da wasu yara da ya kaiwa dauki, dama hoton ya jawo cece-kuce inda da dama mutane sukace ai yayai hakanne saboda siyasa ta fara matsowa dan ya samu kuri'ar mutane, amma ya musanta hakan. Hoto na biyu Gwamnan jihar Imone, Rochas Okorochas shima yana tare da wani yaro wanda da alama taimakonshi zaiyi, hoto na uku, tauraron dan kwallon kafa, Cristiano Ronaldone shima da wani yaro, hoto na hutu, Jarumar fim din hausace, Hadiza Gabon take bayarda taimako.



Bello yace wadannan taimakon da mutanennan suka bayar zai iya zama har zucine zai kuma iya zama na nunawa Duniyane ta gani, amma soyayya ta gaskiya itace ka bayar da kyauta ba tare da kana tunanin samun wani abu daga gurin wanda ka yiwa kyautarba.

Haka kuma yace kyautar 'yan siyasa ta neman kuri'ace a gurin mutane, amma kyautar 'yan kwallo da sanannun mutane(kamr 'yan fim, mawaka da sauransu) suna yintane saboda tsabar soyayya(harzuci).

No comments:

Post a Comment