Pages

Sunday 20 August 2017

Tsohonnan zai baka tausai ya kuma birgeka

Allah sarki a yayin da wasu matasa masu matattar zuciya suke sata ko kuma zaman kashe wando a bakin titi ko kuma kaga katon Allah wata'ala wai yana rokonka kudi(bara) ko kuma wasu tsofaffi masu bara duka dai masu neman dalilin a tausaya musu a basu kudi ba tare da sun sayar da komai ba ko kuma sunyima mutum aikin komai ba, kuma lafiyarsu kalau, da sunan bara, ya kamata su karfafa zuciyarsu a yayin da sukaga wannan bawan Allahn tsohon.

Ayi hakuri ina cikin tafiyane akan titi kuma inada wani uzuri shiyasa na dauki hoton be fito sosaiba, wannan tsohone tukub kamar yanda ake iya gani amma be dauki koko yana baraba, ya samu sana'a, irin farar takardar gogegogece da ake ajiyewa a mota tsohon yake sayarwa.



A gaskiya tsohon ya birgeni sosai lura da wasu tsofaffi irinshi da suke bin tituna da layuka suna bara amma be karayaba ya dauki wannan sana'ar, muna fatan Allah yasamai albarka a ciki ya kuma sa wadanda suke da matacciyar zuciya, musamman matasa su karfafa su tashi su nemi na kansu dalilin wannan.



No comments:

Post a Comment