Pages

Tuesday 14 November 2017

Najeriya ta lallasa Argentina da ci 4-2 a wasan sada zumunta da suka buga a Rasha: Aguero ya na can gadon asibiti bayan da rashin lafiya ta kamashi ana cikin wasan

Argentina Nigeria
'Yan wasan kwallon kafa na Najeriya, Super Eagles sunyi abin yabo a yau Talata a wasan sada zumunta da suka buga da kungiyar kwallon kafa ta kasar Argentina a can kasar rasha, Super Eagles sun lallasa Argentinawan da ruwan kwallaye har hudu yayin da Argentinan ke da ci biyu.


Da farkon wasan dai kamar Super Eagles ba za tayi nasara ba, domin har zuwa mintuna 44 na farkon rabin lokaci, Argentinarce ke cin Najeriya kwallaye biyu wadanda Ever Banega da Sergio Aguero suka zura, ana saura minti daya aje hutun rabin lokaci Najeriya ta samu zura kwallo ta hannun Kelechi Ihaenacho a bugun tazara.

Bayan an dawo hutun rabin Lokaci Najeriya ta farke kwallayen da aka ci ta gaba daya har ta kara guda biyu akai ta hannayen Alex Iwobi, wanda yaci kwallaye biyu da da kuma Brian Idowu.

Wasan dai ya kayatar sosai kuma 'yan wasan Super Eagles sunyi bazata, duk da cewa dama ita kwallo sai an tashi kamin asan ainihin sakamako.

A wani labarin kuma Aguero yana can a gadon asibiti bayan da rashin lafiya ta kamashi ana tsaka da wasan Najeriya da Argentinar kamar yanda Tyc Sport ta ruwaito. 

No comments:

Post a Comment