Pages

Saturday 2 December 2017

"Halayen wannan abokiyar tawa sukasa na shiga addinin musulunci">>inji inyamura data musulunta, A'ishat Obi

A kwanakin bayane wata Inyamura me suna A'ishat Obi data amshi addinin musulunci ta fito ta bayyanawa 'yan uwanta Inyamurai da Duniya cewa addinin na musulunci ya samu kafuwa a yankin Inyamuran kuma tana kira ga 'yan uwanta da suka amshi musulunci dasu tashi tsaye su nemi ilimin addinin.
A yau kuma A'isha, wadda ke sanye da hijabi a wannan hoton na sama ta bayyana abokiyarta, me sanye da gyale, cewa tana daya daga cikin mutanen da kyawawan halayensu ya jawo hankalinta zuwa shiga addinin na musulunci.


A'isha ta kara da cewa wannan 'yar uwatace, kai tamafi karfin 'yar uwa a gareni domin tana daga cikin wadanda kyawawan halayyarsu ya jani na amshi addinin musulunci, kuma ina fatan gamuwa da ita idan Allah ya tashemu kiyama,  A'isha tayi fatan cewa Allah ya bata ikon amfanar da mutane itama.

No comments:

Post a Comment