Pages

Tuesday 19 December 2017

Jamila Abubakar Sadik Malafa, Mace ta farko daga Arewa data kai mukamin Janaral a aikin sojan ruwa

A jiya litinin hukumar sojan ruwa ta Najeriya suka karawa mace ta farko 'yar Arewa Jamila Abubakar Sadik Malafa girma daga kaptin zuwa Commodore mukamin da aka bayyana a matsayin daidai yake da birgediya janaral a sojan kasa, wannan ya baiwa Jamila damar zama mace ta farko daga yankin Arewa data taba zama janaral me tauraro daya.


  
Me kula da harkar tsaretsare na shalkwatar hukumar sojan saman dake Abuja Rerar Admiral Henry Babalola ya bayyana cewa ba karamin abin alfhari bane mutum yakai mukamin da Jamila takai a aikin sojan ruwa ya kuma kara da cewa mata 'yan kadanne suka taba kaiwa ga wannan mukami.
Ya bayyana cewa Jamila ta samu horaswa da kwasa kwasai da yawa kamin takai wannan mukami, kamar yanda jaridar Daily Trust ta ruwaito, kuma wannan mukami data kai ya kamata ya karawa sauran mata dake cikin aikin sojan sama kaimi su tabbatar da cewa zasu iya kaiwa ga kowane irin matsayi.

Jamila ta tabbatar da cewa itace mace ta farko data taba kaiwa wannan matsayi a Arewacin Najeriya kuma wannan zaisa ta kara kaimi wajan yiwa Najeriya hidima tukuru.

An haifi jamila a karamar hukumar Gombi dake jihar Adamawa a shekarar 1965 kuma ta fara aiki da hukumar sojan ruwan Najeriya a shekarar 1988.

Muna mata fatan Alheri.

No comments:

Post a Comment