Pages

Thursday 19 April 2018

Koci da 'yan wasa biyu sun tsere cikin kasar Australia yayin da ake wasan Commonwealth saboda basu son dawowa gida Najeriya

Shugaban hukumar wasan daga abubuwan nauyi ta Najeriya, Muhammad Yahaya ya bayyana wani abin takaici daya faru a kasar Australia inda ake wasannin Commonwealth Games, wani kocine da yan wasa biyu suka tsere suka shiga gari, watau basu son dawowa Najeriya.



Da yake hira da jaridar Vanguard Muhammad ya bayyana cewa wannan abin takaicine ace wai koci guda shima yabi sahun 'yan wasan inda suka tsere daga gurin wasan suka shiga gari saboda basu son komowa Najeriya.

Ya kara da cewa idan su 'yan wasa sun yi haka ai shi koci kamar ubane a gurinsu be kamata ya biye musu ba.

No comments:

Post a Comment