Pages

Saturday 8 September 2018

A karshedai Shekarau ya koma APC: Shin menene matsayin wakar malama ya ci kudin makamai da Rarara yamai?

A karshe dai bayan tattaunawa da akayi tsakanin shugaban APC, Adams Oshiomhole da gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da tsohon gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau, shekarau din ya fito ya bayyanawa Duniya cewa ya koma APC.


Gidan talabijin na Channels ne ya ruwaito da wannan labari inda yace Shekarau din ya bayyana mishi haka bayan ganawar da yayi da shuwagabannin APCn a gidanshi.

Saidai wani lamari da mutane ke ta tattauna akai, musamman a shafukan sada zumunta da muhawara na yanar gizo, shine ina matsayin wakar da mawakin Rarara ya yiwa Shekarau ta Malam ya ci kudin makamai, menene matsayinta yanzu?

Siyasa kenan, saidai a jira nan gaba aji idan mawakin zai sake yin wata wakar tashi, shin zai yabi Shekarau dinne ko kuwa?

No comments:

Post a Comment