Pages

Sunday 7 October 2018

Uba Sani ya lashe zaben fidda gwani na dan takarar sanatan Kaduna ta tsakiya a karkashin jam'iyyar APC

Mai baiwa Gwamnan Jihar Kaduna shawara akan harkokin Siyasa Malam Uba Sani, yayi nasarar lashe zaben fidda gwani na Dan takarar Majalisar Dattawa mai wakiltar Mazabar kaduna ta tsakiya da gagarumin rinjaye. 



Da yake sanar da sakamakon zaben wanda ya gudana a Katafaren zauren taro na tunawa da tsohon Shugaban kasa Umaru 'Yar'aduwa dake Kaduna, Farfesa Edie Floyid Igbo daga uwar Jam'iyyar APC ta kasa, ya bayyana cewar Malam Uba Sani yayi nasara akan sauran abokanan takarar shi su hudu, wato Sanata Shehu Sani, da tsohon Sanata Sani Sale, da Malam Shamsusdeen Giwa, da Honorabul Usman Ibrahim, inda sakamakon zaben ya nuna cewa Malam Shamsusdeen Giwa ya samu kuri'a 6 ne, inda Sanata Shehu Sani ya tsira da kuri 'a 15, shi kuma tsohon Sanata Sani Sale ya samu kuri'a 55, inda Usman Ibrahim ya samu kuri'a 129, yayin da Malam Uba Sani ya samu kuri'a Dubu Biyu da Tamanin da Takwas. 

An dai gudanar da zaben lafiya cikin kwanciyar hankali, inda wakilan Jam'iyyar daga Kananan Hukumomi Bakwai dake yankin suka halarta Mazan su da Matan su suka jefa kuri'ar, sai dai tun da fari Sanata Shehu Sani wanda ya sha kaye a zaben, ya fitar da takardar sanarwa wacce aka rarrabawa manema labarai ita, inda ya bayyana nesanta kanshi da wannan zabe wanda ya kira shirmen El Rufa'i. 

Indai Jama'a basu mance ba uwar Jam 'iyyar APC ta kasa karkashin jagorancin Shugabanta Adams Oshoimole ta ayyana sunan Shehu Sani a matsayin halastacen Dan takarar Sanata a yankin, lamarin da ya haifar da sa toka sa katsi a jihar, har Gwamna El Rufa'i ya garzaya Abuja wajen Shugaba Buhari akan batun, bayan dawowar Gwamnan ne aka tsara gudanar da wannan zabe wanda ya ba Uba Sani gagarumar nasara, shi kuma Sanata Shehu Sani ya sha munmunan kaye.
Rariya.

No comments:

Post a Comment