Pages

Monday 19 November 2018

Maraya na taso kuma har tallar itace na yi>>Atiku Abubakar

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya fara yakin neman zabenshi yau, Litinin ta shafinshi na sada zumunta inda ya fara da bayar da labarin cewa ya taso maraya kuma har sayar da itace yayi.


Yace ya sayar da itace a kan titunan garin Jada dake Adamawa amma Allah, ta sanadiyyar Najeriya ya daukakashi.

Yace idan Najeriya ta bashi irin wannan damar ya kai yanda yake a yanzu to shima yana da aikin gyara Najeriyar yanda zata baiwa kowane danta irin waccan dama.

Yayi kira ga 'yan Najeriya da su bishi akan wannan tafiya ta samar da rayuwa me kyau.

Yace idan aka zabeshi zai taimakawa kananan da matsakaitan masana'antu miliyan 50.

Yace wannan tsari zai samar da ayyuka miliyan 2.5 sannan cikin shekaru 2 mutane miliyan 50 zasu fita daga kangin talauci.

Yace kuma akwai wani tsari da zai fito dashi na horas da mata da maza miliyan daya duk shekara akan sana'o'i daban-daban.

Yace akan maganar shirinshi na canja fasalin Najeriya kuma zai samar da yanayin da jihohi da gwamnatin tarayya zasu samu kudin shiga fiye da da.

Ya kara da cewa ga wanda ke so ya karanta tsare-tsaren nashi zai iya yin haka a shafinshi na Atiku.org.

No comments:

Post a Comment