Pages

Friday 29 March 2019

Buhari ya kaddamar da Tsarin Fanshon ga Masu Kananan Sana’o’i

Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da tsarin fansho na masu kananan sana’o’in da ba su dogara da aiki a karkashin gwamnati ko kamfanoni ba.


An kaddamar da shirin a dakin taro na Fadar Shugaban Kasa, yau Alhamis a Abuja.

Ya kaddamar da shirin inda a farko ya yi aikin sa-ido wajen yi wa wani mai sana’ar tuka A Daidaita Sahu, mai suna Sagir Shawai, yin rajistar tsarin fanshon.

Shawai ya na sana’ar tuka Keke NAPEP ne a garin Karu, a karkashin Gundumar FCT, Abuja.

Buhari ya ce an kirkiro shirin ne domin inganta rayuwa da sana’o’in masu kananan kasuwanci da sana’ar dogaro da kai, ba masu aikin gwamnati o aiki a karkashin kamfanoni masu zaman kan su ba.

Daga nan sai ya roki kungiyoyin ‘yan tireda, kungiyoyin ma’aikata na NGO da su hada hannu da gwamnati domin a kara wayar wa mambobin su kai, ta yadda za su fahimci alfanun shirin.

“A shekaru uku baya da suka gabata zuwa yau, mun bayar da lamuni ga manoma da sauran masu sana’o’i. To wannan Tsarin Karamin Fanshon Masu Kananan Sana’o’i kuwa shi ne mataki nag aba.” Inji Buhari a wurin kaddamar da shirin.
Premiumtimeshausa.


No comments:

Post a Comment