Pages

Thursday 28 March 2019

Karya Magu yake babu gwamnatin data kai ta Buhari satar dukiyar kasa>>Jonathan

Bayan da shugaban hukumar hana yiwa arzikin kasa zagon kasa, EFCC, Ibrahim Magu yayi zargin cewa daga shekarar 2011 zuwa 2015 kamfanoni da wasu mutane 32 sun sace zunzurutun kudi har tiriliyan 1.3, tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan wanda a zamaninshine akayi wannan sata da Magu ya zarga yace ikirarin na Magu karyane.



Da yake mayar da martani ta hannun tsohon hadiminshi, Reno Omokry, tsohon Shugaban kasa, Jonathan ya bayyana cewa Magu karya yake akan wadannan bayanai daya fada kuma wannan ba shine karin farko da ya taba yin hakan ba.

Ya kara da cewa kwanaki kadan kenan da kasar Amurka ta fitar da rahoton dake cewa, har yanzu Najeriya na ruwa tsundun akan maganar rashawa da cin hanci, sannan an mayar da wasu 'yan lele, shafaffu damai akan yaki da rashawa da gwamnatin Buhari ke yi, maimakon ya mayar da hankali akan wannan batu shine zai kama fadin maganar da babu hujja a cikinta.

Yaci gaba da cewa rahoton Transparency International ya nuna cewa, a mulkin Buhari an fi yin cin hanci fiye dana Jonathan, sannan a mulkin Jonathan Najeriya ta fara fita daga kallon da ake mata na kasar cin hanci da Rashawa amma a lokacinsu Buhari sun mayar da ita ruwa.

Yace a mulkin Buharine aka dawo da babban barawo, Abdulwasiu Maina cikin gwamnati aka kuma bashi karin girma har sau biyu.

Yace kuma a lokacin Buharine shugaban kamfanin mai na kasa, NNPC ya bayar da kwangila ba bisa ka idaba ta zunzurutun kudi har dala biliyan 25 wanda wadannan kudin zasu isa a biya ma'aikatan kasarnan miliyan daya mafi karancin albashi na dubu 30,000 da ake ta fama akai Har tsawon shekaru 4.

Yace kuma kiri-kiri aka ga motar kudi ta shiga gidan jigo a APC, Bola Ahmad Tinubu kuma ya fito yace Eh nashine kuma motar cike take da kudi amma maimkon Magu ya mayar da hankali kan irin wadannan matsalolin dan magancesu sai ya ke siyasantar da aikin EFCC wanda be kamata ba

No comments:

Post a Comment