Pages

Monday 20 May 2019

Abin da ya sa aka hana yin tashe a Kano



JIhar Kano
Yayin da ake cikin kwanaki na tsakiyar watan azumin Ramadana, tuni tashe, wanda ke daya daga cikin al'adun da suka shahara a kasar Hausa ya kankama a sassa daban-daban na jihohin arewacin Najeriya da ma kasashe masu makwaftaka.


Sai dai a jihar Kano wadda take a matsayin daya daga cikin manyan yankuna na kasar Hausa, abin ba haka yake ba.
Domin kuwa kamar yadda ta faru a wasu shekarun baya, a wannan karo ma hukumomi a jihar sun haramta gudanar da wannan al'ada mai dinbin tarihi.
A yanzu haka tuni rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar ta Kano ta ce za ta dauki tsattsauran mataki kan duk wanda aka kama ya taka dokar hana yin tashe a jihar.
DSP Haruna Kyawa, mai magana da yawun rundunar 'yansanda a jihar ya ce jami'an 'yan sanda na yin sintiri a cikin dare domin tabbatar da cewa ba a bari masu neman tayar da fitina sun cimma burinsu ba.
Ya ce "ba wai tashen ne laifi ba, a'a. Amma bata gari da suke bin 'yan tashen suke fakewa da haka suke yin kwace da sauran miyagun laifi shi ne ba ma so."
Ya kuma kara da cewa rundunar za ta rika sintiri a lungu da sako na jihar daga lokacin sallar magariba zuwa karfe goma na dare don kama masu karya doka.
A lokacin tashe dai yara da manyan mata da maza ne kan yi shiga iri-iri na domin aikewa da sakonin daban-daban da kuma nishadantar da mutane ta hanyar barkwanci da kuma kade-kade da wake-wake.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment