Pages

Wednesday 22 May 2019

Shugabar kotun daukaka kara ta janye daga shari'ar zaben shugaban kasa

Shugabar babbar kotun daukaka kara ta Najeriya, Zainab Bulkachuwa, ta janye daga shugabancin kotun da ke sauraron karar da dan takarar jam’’iyyar PDP Atiku Abubakar ya shigar, inda yake kalubalantar nasarar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a zaben shugabancin kasar da ya gabata na watan Fabarairu.



Matakin na Bulkachuwa, na daga cikin bukatun da dan takarar adawar na PDP Atiku Abubakar ya gabatar, bayan da yayi zargin cewa kotun sauraron kararrakin zaben ba za ta yi masa adalci ba, a karkashin Bulkachuwa.

Kafin daukar matakin da Bulkachuwa ta yi, sai da tawagar alkalai 5 masu sauraron shari’ar zaben na shugaban kasa suka yi watsi da zargin na Atiku Abubakar, inda suka ce babu dalilin da zai sa su yi wa dan takarar rashin adalci, sai dai duk da haka maishari’ar ta bayyan janyewa daga kotun sauraron kararrakin.

Yayin bayyana matsayinsu kan zargin na dan takarar PDP a madadin takwarorinsa, mai shari’a Olabisi Ige, ya jaddada cewa alakar da ke tsakanin mai shari’a Bulkachuwa da mijinta zababben Sanata Adamu Bulkachuwa, da kuma danta Aliyu Abubakar dukkaninsu ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki, ba za ta yi tasiri wajen sanya Zanab Bulkachuwa yin rashin adalci ga Atiku Abubakar ba, kan kalubalantar nasarar Buhari da yake yi.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment