Pages

Tuesday 21 May 2019

Trump yayi barazanar rusa Iran baki daya

Shugaban Amurka Donald Trump yace muddin Iran ta kuskura ta kai hari kan muradun Amurka, Amurkan za ta rusa ta baki daya.



Gargadin na Trump kunshe ne cikin sakon da ya aike ta shafinsa na twitter, inda yace kaiwa muradin kasar hari zai bada dama wargaza Iran baki daya, dan haka shugaban ya gargadi kasar da ta daina yi wa Amurka barazana.

Tankiya tsakanin kasashen biyu tayi kamari ne bayan da Amurka ta tura jiragen ruwanta masu dauke da jiragen saman yaki yankin tekun Fasha.

Sai dai wasu rahotannin sun nuna rarrabuwar kawuna tsakanin manyan jami’an gwamnatin Trump kan yakin, yayin da ake zargin mai baiwa Trump shawara kan harkokin tsaro John Bolton da tunzira Amurka domin kaiwa kasar ta Iran hari.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment